Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti As Abna ya habarto maku cewa: shugaban Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibrahim Ya'aqub Alzakzaky, ya tabbatar da cewa, Guguwar Al-Aqsa, tun farkonta, wata nasara ce ga Gaza bisa la’akari da cewa dukkan Mutanen da suke goyon bayan Falasdinu sun kammala karatunsu ne a makarantar Imam Husaini.
A wajen rufe Maukibin kiran Al-Aqsa da aka gudanar a kan hanyar masu ziyara a Karbala mai alfarma, Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: Duk da irin goyon bayan da mamaya ke samu daga manyan kasashen duniya, ya zuwa yanzu ba ta iya yin komai ba illa kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Bisa la'akari da cewa Palasdinawa na fuskantar girman kan duniya baki daya.
Shaikh Al-Zakzaky ya jaddada cewa, guguwar Al-Aqsa, tun kafuwarta, wata nasara ce ga Gaza, yana mai cewa: haduwarmu ta yau a kan hanyar Karbala shaida ce da ke nuna cewa juyin juya halin Husain ya yi nasara.
Ya kara da cewa Imam Husaini ya samu nasarar juyin juya halinsa wanda ya sauya tunanin duniya, yana mai nuni da cewa dukkanin wadannan jama'a da ke kan hanyar zuwa Karbala suna amsa kiran Imam Husaini ne.
Shaikh Al-Zakzaky ya yi la'akari da cewa: Wadannan tarin jama'a shaida ne na nasarar da jini ya samu a kan takobi, yana mai cewa: Ina tilastawa kaina in ga abin da ke faruwa a Gaza a kowace rana duk da irin munin yanayin da ganin ya ke da.
Shaikh Al-Zakzaky ya jaddada cewa: Dukkanin masu goyon bayan Falasdinu sun fito ne daga makarantar Imam Husaini, inda ya ce gwagwarmaya da imanin Palasdinawa ya sauya akalar duniya kan Musulunci, yana mai jaddada cewa alamy sun tabbatar da gushewar "Isra'ila" da samun nasarar Falasdinawa da Gaza.